Rahotanni na nuni da cewa wata dadaddiyar bishiyar kuka da ta kwashe shekaru masu yawan gaske a wata gona dake yankin garin Kofa an wayi gari anga ta bace sama ko kasa an nemeta an rasa.
B Imam
Hakan ya zo ne a daidai lokacin da wani bawan Allah mai unguwar garin na kofa yaje gonar tasa domin yin kewaya da niyar fara gyaran gonar ganin damina tana shirin kankama.
Da yake jawabi ga manema labarai shedan gani da ido yace Kukar ta sami fiye da shekara shida a kwance Kuma ba wani me ya kwantar da it ba amma a wannan karo said suka nemeta suka rasa duda babu wata alama ta cewa an sare tane an kwashe.