BABIN SIYASA DIMUKURADIYYA.

Duk Danmajalisar Jiha ko na Tarayya a Nigeria da ya yi wa’adi uku cur a jere (consecutively) a majalisa, ga shawara alumma su canjashi da sabo, kila sabon da za su zaba ya zo musu da wasu kudurce-kudurce da tarin alheran da Shi Dantazarcen sam! Bai zo musu da su ba ko sam! Ba zai taba kawo musu ba.

Daga Musa Mudi Dawakin Tofa.

A don haka wasu masharhanta da masu fashin baki, lokaci bayan lokaci suke tata yin kira ga majalisun kasar nan da suka shude dama na yanzu cewa “lokaci ya yi da ‘Yanmajalisun kasar nan za su kayyadewa kansu da kansu dokar wa’adin mulki (tenure) kamar na Gwamnoni dalilinsu, shi ne a Nigeria alumma tana ta karuwa, suma masu son su dana shugabancin siyasar suna ta karuwa matuka “.

Tambaya me ne ne dalilin da yasa aka mayar da wa’adin shugabanci Jami’oin kasar nan (University Vice Chancellor’s/University Minister’s) zuwa Zango daya tak wato su rika yin shekaru 5 amma babu tazarce a maimakon 4 ,

saboda suma masu son shugabacin musammama Furofesoshi da Daktoci suna ta karuwa a Jami’oi.
Me ne ne ra’ayinku?

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments