Aston Villa ta nada Unai Emery a matsayin sabon kociyanta, domin maye gurbin Steven Gerrard wanda ta kora ranar Alhamis.
Tsohon kocin Arsenal, wanda ke jan ragamar Villareal, zai fara aiki ranar 1 ga watan Nuwamba.
Villa ta biya Villareal £5.2m kudin kunshin kwantitagin mai shekara 50, wadda aka gindaya ga duk mai son daukar shi idan wa’adinsa bai cika ba.
Kociyan rikon kwarya Aaron Danks shi ne zai ja ragamar Aston Villa wasan Premier da za ta kara da Newcastle a karshen mako.
Villa ta kori Gerrard bayan da Fulham ta yi nasara da ci 3-0 a wasan Premier League ranar Alhamis, wanda ya ci wasa biyu kacal a bana.