Najeriya ta zama kasa ta 103 cikin jerin kasashen 121 da aka ce suna fama da matsalar yunwa, kamar yadda shugaban Bankin Ci gaban Afrika AFDB Akinwumi Adesina ya bayyana.
Ya bayyana hakan lokacin da ake kaddamar da wani shiri na musamman kan cibiyoyin sarrafa albarkatun noma a Najeriya a ranar Litinin a Abuja.
Ya ce Afrika na fuskantar gagarumin kalubalen karancin abincin da take bukata, yayin da mutum miliyan 283 ke fama da yunwa duk shekara. Ya kara da cewa Afrika na da yanayin noma da yakai kashi 65.
Adesina ya ce “kamar yadda kididdigar yunwa ta duniya ta 2022 ta bayyana, wadda aka saki mako guda baya, Najeriya na matsayi na 103 cikin jerin kasashe 121 da ke fama da yunwa a a duniya.
“Babu wata hujja ta fuskantar yunwa, Najeriya na da kasar noma tana da hekta miliyan 34 ta noma.” in ji Adesina.