Asalin kalmar magani ranar hausa ta duniya Dr.mamman dorayi

A yayin zantawar mu da Dr.mamman dorayi garejin kamilu shugaban cibiyar hada magunguna nan na dauri yace maganin gargajiya dana musulinci ya samo asali ne tin tale tale ta yadda ya ambata cewar duk wani gida da kagani a kasar hausa suna da nasu gadon da suka shahara dasu kamar wanzanci kira yar mai ganye gidan sarkin ruwa dadai sauran su

Daga wakilin aksammedia B.imam

Dr.mamman ya kara da bayyana irin tasirin da maganin gargajiya keda shi na murkushe kuta baki dayan ta muddun anyi amfani da ilimi wajan sarrafa magani da kuma tabbatar da cutar mara lafiya kamin a dora shi akan magani

Ya bayyana cewar kamfanin su yana amfani da kayan gwaje gwaje na zamani domin auna yanayin yadda cutar ta kama majinyaci

ya bayyana irin yadda suke da alaka mai kyau da asibitocin da cibiyoyin kiwan lafiya wajan ganin Al’ummar annabi sun kasance da ingantacciyar lafiya

Daga karshe ya fayyace yadda kalmar magani ta samu asali da cewar muddun kaje wajan mai magani idan ya baka sai yace “jeka ma gani” dake malam bahaushe nada hikima sai hade jimlolin suka bada kalma guda wato magani

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments