Birnin Kano ya cika da Baki daga sassa daban daban na ciki da wajen kasar nan domin shaida Daurin Auren ‘yar Sarkin Kano Rukayya Aminu Ado Bayero.
Da yake adduar Daurin Auren babban limamin Kano Professor Muhammad Sani Zaharadeen ya ce Ango Amir UK Umar ya biya Sadakin Amaryarsa Rukayya Aminu Bayero naira Dubu Dari biyu.
Daga wakilin mu B.imam
Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne ya Zama waliyin Rukayya Aminu Ado Bayero, Wanda shine ya bayar da Aurenta ga Amir UK Kibiya.
Sarakuna daga sassan kasarnan da Gwamnoni da manyan Masu kudi da Yan kasuwa na cikin kasar nan da wajenta sun halarci taron Daurin Auren.
Mun samu wannan labari daga Abubakar Balarabe Kofar Naisa mai magana da yawun masarautar kano