Masarautar jihar Kano ta Sha alwashin baiwa kungiyar tallafawa masu larurar cutar amosanin jini gudunmawar da ta dace domin wayar da kan alumma musammancin yin gwaji kafin aure domin kaucewa kamuwa da cututtuka daban daban.
Maimartaba Sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ne ya tabbatar da hakan a lokacin da kungiyar ta Kai masa ziyara da kuma bashi lambar girmamawa a fadarsa dake nan kano.
Maimartaba Sarkin yace yana umartar kungiyoyi masu zaman kansu da shugabanni masu rike da masarautun gargajiya da hukumomin Lafiya da sauransu da su tabbata cewa sun baiwa irin wadannan kungiyoyi hadin kai wajen ganin ta wayar da kan alumma amfanin yin gwaji kafin aure.
Aminu Ado Bayero, ya bayyana farin cikinsa bisa jajircewar kungiyar ta yadda kuma ya ga kungiyar duk matasa ne ke jagorantarta, kasancewar matasa sune kashin bayan kowacce tafiya.
Sarkin kuma godewa Shugabancin kungiyar karkashin jagorancin Alh Maharazu Ibrahim Adamu Gizina, bisa jajircewar da gudunmawar da yake bayarwa wajen wayar da kan alumma musammancin yin gwaji kafin aure, inda kuma, ya yabawa kungiyar bisa karramawa da ta yi masa da bashi matsayin uban wannan kungiya ta taimakawa masu larurar cutar amosanin jini ta jihar Kano.
A jawabinsa tun da farko shugaban kungiyar Alh Maharazu Ibrahim Adamu Gizina, yace sun kaiwa Maimartaba Sarkin
Ziyarar ne domin neman Masarautar ta tallafawa yunkurin kungiyar wajen ganin an baiwa masu ungunwanni da dakatai da sauran hukumomi su baiwa kungiyar hadin kan
daya dace wajan wayar da kan alumma yin gwaji kafin aure da kuma baiwa sarkin lambar girmamawa ta musamman dangane da gudunmawar da yake bayarwa a jihar nan.
Maharazu Ibrahim yace kungiyar zata ci gaba da wayar da kan alumma yadda yakamata a lungu da sako na birni da kankara da kananan hukumomi dake jihar nan
Amfanin yin gwaji kafin aure.
Haka zalika, ya yabawa Maimartaba Sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero, bisa dama da ya baiwa kungiyar da shawarwarin da suka kamata musamman domin wayar da kan alumma musammancin yin gwaji kafin aure a jihar Kano.
Yace kuginyar a shirye take wajen ganin ta ci gaba da gudanar da harkokinta kafa da kafa da Masarautar jihar Kano
Kamar yadda Maimartaba Sarki Ya umarta domin kawo ci gaba da bunkasar tattalin arzikin jihar Kano ta fannoni da dama.