Shugaban kasar Türkiye, Recep Tayyip Erdogan ya tattauna da Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ta wayar tarho.
Erdogan ya bayyana cewa, ya kamata a ci gaba da raya hangen nesa ta hanyar diflomasiyya a kowane hali.
Kazalika ya ce a shirye suke su ba da duk wata gudunmawar da ta dace wajen kawo karshen yaki kasar da Russia ta hanyar yin shawarwarin da suka Dace.