Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna yatsa ga ƙasashen Yamma yana mai kiran su da ‘munafukai” saboda gazawarsu wajen ɗaukar matakan da suka dace kan sauyin yanayi.
“Da yawa daga cikin takwarorina [shugabannin ƙasa] na nuna damuwa game da munafurcin ƙasashen Yamma da gazawarsu wajen kasa ɗaukar matakin da ya dace,” a cewar shugaban cikin wata maƙala da ya rubuta wa jaridar Washington Post ta Amurka.
Shugaban ya jaddada cewa shugabannin Turai sun sha nuna gazawa wajen cika alƙawarin samar da dala biliyan 100 don shawo kan “matsalar sauyin yanayi da suka haifar da kansu” ga ƙasashe masu tasowa.
Ya ƙara da cewa daga yanzu ba zai yiwu ƙasashen Turai su dinga tsara yadda ya kamata ƙasashen Afirka za su yi amfani da ma’adanan da suke da su ba.
“Kar ku faɗa wa ‘yan Afirka yadda ya kamata su yi amfani da arzikinsu. Da a ce Afirka za ta yi amfani da dukkan arzikin iskar gas da take da shi a rumbuna, wanda shi ne mafi inganci ga muhalli, hayaƙin da ke gurɓata yanayin duniya zai tashi daga kashi 3 cikin 100 zuwa 3.5.”
Afirka na fitar da kashi kusan uku ne kacal na hayaƙi mai gurɓata muhalli a duniya baki ɗaya amma tana cikin nahiyoyin da suka fi kowace fuskantar bala’in sauyi n yanayin.