Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi Allah wadai da sakamakon binciken da majalisar dokokin kasar ta gudanar kan tarzomar da magoya bayansa suka yi a shekarar da ta gabata inda yace hakan kama karya ce kawai aka yi masa.
A cikin sanarwar da Trump ya fitar, ya ce maimakon majalisar ta mayar da hankali kan manyan matsalolin kasar Amurka amma ta kasance yar amshin shata, ta hanyar kawar da hankalin jama’ar Amurka daga matsanancin radadin da suke fuskanta zuwa binciken abinda bashi da amfani ga alummar kasar.
Tun bayan balle tsaron majalisar da Yan jagaliyar Trump suka aiwatar Abara majalisar ta kafa Kwamitin gudanar da bincike kan lamarin inda awannan karo ya gudanar da zaman sauraron korafe-korafe karo na shida da nufin gano dalilin da ya sa aka sami wannan tarzoma daga magoya bayan Donald Trump din a bara.
Sai dai tuni aka yi wasti da guda daga cikin kararraki 62 da kwamitin yakin neman zaben Trump ya shigar, karkashin amincewar mafiyawan alkalan da jam’iyyar Republican ta nada.
Tun da fari Shugaban kwamitin Bennie Thompson a jawabin bude taron tattaunawar da ya gabatar, ya ce duk da cewa Trump ya san cewa ya fadi a zaben, amma ya kekashe kasa ya ki amaincewa, maimakon hakan sai ya fara kaiwa bangaren dimokradiyya hari.