Iyalan Faram sun kaddamar kamfanin takin Zamani na FURSA FERTILIZER COMPANY tare da rarraba Takin ga Manona domin Nomar shekara ta 2022n da muke ciki, a garuruwan Hadejia, Kafin Hausa da kuma kirikasamma dake Jihar Jigawa yankin Arewa maso Yammacin Nigeria.
Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da Kamfanin Takin Zamanin a ranar Litinin, Malam Ahmad Hussain, wanda shi ne ya samar da Kamfanin ya ce, “ muna sa ran Takin zai kara bunkasa harkar Noma da magance yunwar da ake fama da ita da kuma samar da Aiyukan yi a fadin Nigeria”.
Daga wakiln mu B.imam
Ya ce, “yanzu haka sun bayar da tallafin akalla kusan Tan 350 ga kananan Manoma da kuma masu sha’awar fara aikin Noma tin daga tushe”.
Mal. Ahmad ya kuma ce, daga wannan lokacin zuwa ko yaushe Takin zai dinga zuwarwa Manonaman kai tsaye musammanma yankunan da keshan wuyar Noma.
Sannan yayi ikirarin cewa, za su tabbatar sun shiga lunguna da sakunan Jihar dan ganin sun saukakawa Manoman da kuma wadatar da masu bukatar takin ba tare da an wahalar dasu ba.
Sai dai ya bukaci abokan huldar su dasu kulla kyakkyawar alaka da wakilan da zasu dinga kai musu Takin domin a kudu tare a kuma tsira tare.
Mal. Ahmad ya ce, game da tsarin bada bashi kuwa, suna da bam-banci da sauran kamfanoni domin sun samar da hanyoyin biya cikin sauki.
Yunusa Bulama, wani Manomi ne daya samu tallafin, kuma da yake bayyana farin cikin sa ya ce, “ hakika tallafin da aka bamu zaisa mu kara himma akan Nomar da muke yi, wanda daga haka muke sa ran zama masu bayarwa anan gaba muma ”.
Inda ya kuma yabawa Iyalan na Faram, bisa yadda su kayi tunanin samar da Kamfanin a jihar Jigawa.
A cikin wata wasika data samu sa hannun Ahmed Hussain, shugaban Kamfanin ta ce, Kamfanin zai dinga gudanar da Al’amuran sa ne ba tare da an dorawa talakwa kudin Ruwa ba.
Sanarwar ta ce Kamfanin FURSA FERTILIZER COMPANY, zai fi maida hankali ne akan tallafawa kananan Manoma da ‘yan Kasuwa domin a kara samar da kasuwanci na gari.
Daga bisani sanarwar ta ce, za su martaba bukatun Mutane dana abokan cinikayyar su, sannan Kamfanin ya ce, za su daga darajar Masu Nomar Shinkafa da sauran nau’in Abincin Tsaba a fadin jihar Jigawa dama kasa baki daya.
A karshe sanarwar ta lashi kakobin ganin Manoma sun zama Lamba daya a fadin Nigeria.