Daga Abdulhamid isah D/Z
Kwamishinan yan sanda na jihar kano CP mamman dauda ya gardadi jami’an Rundunar yan sandan jihar Kano da su guji shiga harkokin siyasa musamman a lokacin da ake kara tunkarar kakar zaben 2023.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci bude ofishin yan sanda da ke kofar kudu a gidan mai martaba sarkin kano a yau alhamis.
” Kamata ku sani ku baku da jam’iyya ba ruwanku da APC ko PDP ko NNPP ku jam’iyyar ku itace rundunar yan sanda ta kasa ita kuma ta kowa ce, ba ta wata jam’iyya ba”
CP Mamman Dauda ya kara cewa duk jami’in dan sandan da aka kama ya tsunduma sabgakar siyasa ko kuma ya nuna goyan bayan wata jam’iyya to babu shakka za hukunta shi daidai da tanadin dokar aikin dan sanda.
Har wa yau kwamishinan yan sandan yace aikin dan sanda ya hana kowanne Jami’in yan sanda ya biciki wayoyin Wanda aka kama da laifi domin ganin kudaden da suke cikin wayoyinsa domin su karbi na goro a hannunsa yin hakan laifi ne a hukuman ce .
Hakazalika yakara da cewa yakamata yan sanda susani cewa sufa wakilan mutane ne kuma yakamata suyi kokarin ganin sunyansa soyyyar aikinsu a tsakanin jama’ar jihar Kano