Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa tace tayi asarar naurar tantance katin zabe kimanin guda 9,836 a jerin harehare guda 42 da aka kaiwa hukumar cikin shekaru uku a fadin kasar nan.
kazalika tayi asarar rayukan maaikatanta da suka hada da masu aikin zabe da jamian tsaron hukumar kimanin mutane 1,149 a zaben da ya gudana daga shekarar 2011, 2015 da 2019, da kuma tarin kayaiyakin zabe na makudan kudade da suka salwanta a sakamakon rashin kyawun yanayi datsaro mai inganci.
INEC tace ko a makon da ya gabata Jamiin ta mai suna Anthony Nwokorie ya rasa ransa a hanun yan bindiga yayin da yake rijistar zabe a karamar hukumar Ihitte Uboma a jihar Imo.
Last Friday, an INEC worker identified as Anthony Nwokorie, was shot dead by gunmen while conducting the continuous voter registration in the Ihitte Uboma Local Government Area of Imo State.
INEC ta Kara da cewa akwai yanzu hukumar a cike take da fargaba da razani dangane da zabe mai zuwa na 2023.
Wani maikacin Hukumar ta IINEC dake jihar Akwa Ibom Mike Igini, a zantawar sa da manema labarai ya gargadi jama’a da su gujewa du wata tashintashina musamman a hukumar ta INEC.
kazalika yace yana mai shedawa yan Najeriya Hukumar su tana cikakken shiri na bayar da kariya ga jamian ta da kuma kayaiyakin gudanar da aikin zaben na shekarar 2023.