Ecowas zata kai ziyarar aiki na kwanaki biyar kasar Niger.

Kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma ECOWAS ta ce za ta aika wani babban ayari zuwa Nijar don yin nazari kan halin da ‘yan kasashen Afirka ta Yamma ke shiga a kasar lokacin da suke yin kaura zuwa Arewacin Afirka da nahiyar Turai.

Yayin ziyarar ta kwana biyar, ayarin zai gana da hukumomin Nijar da kuma Hukumar kula da Kaura ta Duniya don tattauna ingantattun dabaru masu dorewa na shawo kan matsalolin da ‘yan kasashen Afirka ta Yamma ke shiga lokacin da suke kaura ta cikin Nijar.

Jami’an na karkashin jagorancin shugabar harkokin zamantakewa da bunkasa rayuwar dan’adam a Hukumar ECOWAS, Farfesa Fatou Sow Sarr da wakilai daga kasashe mambobin kungiyar wadanda lamarin ya fi shafa.

Kasashen su ne Guinea da Najeriya da Mali da Senegal da Aburi Kwas da Nijar da Burkina Faso da Laberiya da Gambiya da Saliyo da kuma Benin.

Tattaunawar jami’an za ta fi mai da hankali ne kan mayar da ‘yan ci-rani gida bisa ra’ayin kansu da sake tsugunnar da su a zangonnin ‘yan ci-ranin da suka rasa na-yi a kasar ciki har da tantance ‘yan ci-ranin da suka shiga halin kaka-ni-ka-yi da masu komawa gida don a taimake su.

Ziyarar ta zo ne daidai lokacin da wani rahoton Ofishin Hukumar kula da Kaura ce – Kaura ce ya nuna gagarumar korar ‘yan kasashen ECOWAS akasari daga Aljeriya da Nijar.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments