Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano na ci gaba da Kai agajin gaggawa ga kananan hukumomin da suka samu ibtilain ambaliyar ruwa da rugujewar gidaje wanda ya haifar da rasa rayuka da dukiyoyi.
Shugaban hukumar na jihar Kano Alhaji sale Jili ne ya sanar da hakan azantawarsa da manema labarai a ofishinsa dake nan kano.
Alhaji sale Jili ya bayyana cewar an samu ambaliyar ruwa a wasu kananan hukumomi dake jihar nan tun daga fara zubar ruwan sama a wannan lokaci na damuna da muka shigo.
Shugaban ya kuma bayyana cewar daga cikin kananan hukumomin da ibtilain Ya Shafa akwai karamar hukumar Doguwa da gidaje suka rushe Wanda aka yi asarar dukiya sama da miliyan sabain Sai kuma karamar hukumar kibiya gidaje 188 da asarar dukiyoyin alumma sama da naira miliyan 30.
Shugaban ya kuma kara da cewa a karamar hukumar kiru an samu gidaje 106 da yin asarar Dukiyoyi sama da miliyan 35,sai kuma karamar hukumar Rago an samu rugujewar gidaje da mutuwar mutane biyu, inda kuma mutane uku suka samu munanan raunuka, daganan karamar hukumar Dambatta inda aka samu rugujewar gidaje 443 da mutuwar mutane biyu tare raunata mutum daya Sai kuma asarar Dukiyoyi na kimanin mmiliyan15.
Kazalika yace an samu ruwan sama da kankara karamar hukumar tsanyawa da yayi sanadiyar asarar gidaje guda dari Wanda har yanzu hukumar bata kammala tantance yawan asarar da aka samu ba.
Shugaban ya kara da cewa ya zuwa yanzu hukumar ta kiyasta asarar da aka samu da ta Kai naira miliyan 358.
Daga karshe Shugaban hukumar Kwamared sale Jili yayi kira ga masu ruwa da tsaki da masu hannu da shuni da sauran kungiyoyi masu zaman kansu da su tallafawa yunkurin gwamnatin jihar Kano da kuma Hukumar wajen tallafawa alumma da suka tsinci kansu a ciki.