Masana kimiyya a ƙasar Ecuador sun gano wasu sabbin nau’in kwaɗi shida a ƙarƙashin tsaunukan gabashin ƙasar, waɗanda ke cikin gandun dazukan ƙasar biyu.
To sai dai masanan sun yi gargaɗin cewa duka sabbin nau’ikan kwaɗin da suka gano, an gano su ne a tsakiyar wani ƙasurgumin kurmi da aka sare.
Sanna kuma sun buƙaci a sanya su cikin jerin dabbobin da ke fuskantar barazanar ɓacewa a doron duniya.
Akwai nau’ikan kwaɗi da suka kai 550 da ke raye a yankuna daban-daban, kama daga gabashin Honduras zuwa tsaunukan arewacin Argentina da Brazil.
Colombia da Ecuador na da yawan irin waɗannan nau’ikan dabbobi, waɗanda masana kimiyya ke tunanin cewa akwai sabbin nau’ikan da kawo yanzu ba a iya gano su ba.