An fille kan dan majalisa mai ci a jihar Anambra

Wasu da ake zargi yan bindiga ne sun fille kan  dan majalisa mai wakiltar al’ummar Gwamna Charles Soludo a majalisar dokokin Anambra Okechukwu Okoye,.

Mista Okoye, wanda ke wakiltar mazabar Aguata 2 a jihar Anambra, an sace shi ne tare da mai taimaka masa, Cyril Chiegboka, a ranar Lahadin makon jiya a hanyar Aguluzigbo, a karamar hukumar Anaocha ta jihar.

An ce an jefar da kan sa ne a wani wurin shakatawa na Chisco da ke Amichi, a karamar hukumar Nnewi ta Kudu a ranar Asabar, kwanaki shida bayan da aka sace shi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a daren Asabar.

Ya ce daga baya an tsinci gawar dan majalisar a kan titin Ideani, unguwar Nnobi, karamar hukumar Idemili ta Kudu. Sai dai bai bayyana komai kan makomar mai taimaka wa dan majalisar, Cyril Chiegboka ba, amma akwai alamun mai yiwuwa ma an kashe mataimaki.

Kakakin ‘yan sandan ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Echeng Echeng, ya bayyana kisan dan majalisar a matsayin “abin kunya ga tsoron kasa”

Mista Echeng ya kuma jajantawa ‘yan uwa da abokanan dan majalisar tare da ba da tabbacin cewa ‘yan sanda za su zakulo wadanda suka kashe shi.

Wani faifan bidiyo da ya dauki kan da aka jefar a wurin shakatawa ya bazu a shafukan sada zumunta daban-daban.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments