Wani Dutse a kaasar Indonesia an wayi garin yau da shi Yana feshin wuta Mai nisan kilo mita biyar biyo bayan wata girgizar kasa da ta gudana a yankin Merapi.
Shugaban hukumar kula da ibtilain zaizaya da girgizar kasa na Indonesia, Abdul Muhari, ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace tuni jamian hukumar su sun garzaya domin aikin ceto a yankin.
Kazalika yace kawo yanzu sun kwashe mutane 253 dake kusa Dutsen zuwa nisan tazarar kilo mita bakwai Kuma yace kawo yanzu babu asarar rayuka.
Ya Kara da cewa kimanin tsawon shekaru 12 kenan da makamancin hakan ya faru inda yayi sanadiyar rasa rayukan mutane 347 bayan cetar 20,000.












