Alkalin Alkalai na kasa, Ibrahim Tanko, ya yi murabus daga mukamin sa

Rahotanni na nuni da cewa Ibrahim Tanko Muhammad, Alkalin Alkalan Najeriya ya yi murabus daga mukaminsa.

Tanko, wanda murabus dinsa ya fito fili ne a yau ranar Litinin 27-06-2022, inda aka ce murabus din ya biyo bayan  dalilai na lafiya ne.

Mai shari’a Tanko Bafullatani, an haife shi a ranar 31 ga Disamba 1953 ya zama Alkalin Alkalan Najeriya a ranar 11 ga Yuli, 2019.

Tanko ya fara aiki ne a shekarar 1982, bayan an kira shi lauya a shekarar 1981. A shekarar 1989 aka nada shi a babban kotun majistare ta babban birnin tarayya, mukamin da ya rike har zuwa 1991 inda ya zama alkali a jihar Bauchi a Kotun daukaka kara ta Sharia, ya yi wannan aiki na tsawon shekaru biyu kafin a nada shi a benci na kotunan daukaka kara ta Najeriya a matsayin Justice a shekarar 1993.

Ya rike wannan mukamin na tsawon shekaru goma sha uku kafin a nada shi kujerar kotun kolin Najeriya a shekarar 2006 amma aka rantsar da shi a ranar 7 ga watan Janairun 2007

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments