Daga Sadiq L Hassan
Jam’iyyar PDP a Katsina ta shirya naɗa tsohon sakataren Gwamnatin Katsina, Mustapha Inuwa a matsayin babban direkta da zai jagoranci yaƙin neman zaɓen ɗan takarar Gwamnan Katsina Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke dana shugaban ƙasa Atiku Abubakar a Katsina.
Wani wanda ya san da lamarin ya sheda ma Katsina Post kuma ya nemi a sakaya sunansa.
Wannan matakin yazo bayan ƙasa da mako ɗaya da Mustapha Inuwa ya sanar da komawar shi jam’iyyar PDP tare da ɗinbin magoya bayan shi da ƙungiyoyin dake tare dashi.
Katsina Post ta ruwaito cewa a ranar lahadin data gabata, Mustapha Inuwa, wanda jigo ne a jam’iyyar APC kuma tsohon ɗan takarar Gwamnan Katsina, ya sanar da matakin daya ɗauka da magoya bayanshi na ficewa daga jam’iyyar APC.
Lamarin da ya haifar da cece kuce da al’ummar ke ganin zai zama barazana ga samun nasarar jam’iyyar APC a jih ar Katsina.