Kwararrun Likitoci 500 ne suka bar Najeriya Cikin Shekaru Biyu, inji Kungiyarar.
Daga Walid Y Hari
Kungiyar kwararrun likitoci ta Najeriya ta shaida cewa, akalla kwararrun likotoci 500 ne suka fice daga Najeriya domin kama aiki a wasu kasashen waje. Kungiyar ta ce, likitocin da yawansu ma’aikatan gwamnatin jihohi ne da na tarayya, kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.
Ya ta’allaka laifin ficewar likitoci daga Najeriya ga gwamnatin kasar, inda yace sam gwamnati bata ba da cikakkiyar kulawa ga bangaren lafiya da kuma kula da jin dadin ma’aikata har ma da mutunta su.
Da yake bayyana dalili, ya ce neman cikakken kwanciyar hankali dadin rai ke sa liktocin ke tsallakewa zuwa kasashen da zasu sami tsarin aiki mai dadi. A cewarsa:
“A shekaru biyu da suka gabata, sama da kwararrun likitoci 500 ne suka bar aiki a asibitocin gwamnatoci don komawa aiki a kasashen waje. Dukkan asibitoci gwamnati na karkashin kulawar kwararrun liktoci ne, wanda shine tsari a ko’ina a duniya.