Shugaban Hukumar Kula da zirga-zirgar Ababen Hawa ta jihar Kano, wadda aka fi sani da KAROTA, Hon Dr. Baffa Babba Ɗan’agundi a yau Litinin ya miƙa takardarsa ta sauka daga kan muƙaminsa na Shugaban Hukumar KAROTA ta hannun Muƙaddashin Gwamnan Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna.
Jamiin hulda da jama’a na hukumar KAROTA Nabilusi Abubakar
Ƙofar Na’isa shine ya bayyana Hakan ga manema labarai inda yacs
Hakan ya biyo bayan umarnin da Majalisar Tarayya ta Ƙasa ta fitar kan gyaran Kundin Zaɓe na shekara ta 2022 da cewa, ga duk mai sha’awar yin takara dole ne ya sauka daga kan muƙaminsa wata guda kafin zaɓen Firamare.
A yau ne Shugaban Hukumar ta KAROTA ya miƙa takardar tasa sai dai ya samu umarni daga mai Girma Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje na jinkirta karɓar takardar, tare da umarninsa da ya ci gaba da zama a kan kujerarsa, ya jira umarni na gaba.
Idan ba a manta ba a ranar Lahadi da ta gabata ne shugaban Hukumar ta KAROTA Hon. Baffa Babba Ɗan’agundi ya bayyana cewa yau Litinin zai ajiye muƙaminsa domin tunƙarar al’amuran siyasa gadan-gadan
Shugaban Hukumar ta KAROTA ya bayyana cewa shi mai biyayya ne ga umarnin Gwamna, hakan ta sa ya jinkirta sauka daga kan muƙamin nasa kamar yadda aka bashi umarni.