Bayan jam’iyyar adawa ta PDP ta tsayar da dan takarar ta na Shugabancin kasa daga arewa Sanata Kabiru Ibrahim Gaya yace kamata yayi jam’iyyar APC ta tsayar da Dala nata dantakarar daga kudancin kasar nan.
Gaya ya ce bai wa yankin kudanci takarar shi ne babban alheri da adalci ga APC , kuma a cewarsa zai sa ta ci zabe a 2023.
Wannan na zuwa ne, yayin da rahotanni ke cewa akwai zaman dar-dar a jam’iyyar ta APC gabanin zaben fid da gwani na takarar kujerar shugaban kasa.
Bayan shugaba Muhammadu Buhari ya tara gwamnonin jam’iyyarsu, tare da shaida musu cewa ya zabi wanda zai gaje shi kuma yana son su goya masa baya domin ya samu tikitin tsayawa takara, abin da aka ce bai yi wa wasu gwamnonin dadi ba.
Gaya yace “Ita siyasa, ko duk rayuwar duniya alkawari ce. In ka yi wa dan Adam alkawari to ka cika alkawarin da kayi da shi. An yi alkawari da kudu, sun amince Buhari yayi mulkin shekara takwas, ya kamata kuma a mika musu, domin su ma su yi shekara takwas