Daga Walid Hari
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya gabatar da kasafin kuɗi na 2023 da ya kai naira tiriliyan 19.76 a gaban gamayyar majalisun dokokin kasar ranar Juma’a.
Wannan ne kasafin kuɗi mafi yawa a tarihin Najeriya, inda ya zarta na shekarar 2022 da kashi 15.37 – wanda aka gabatar kan naira tiriliyan 17.13
Kasafin kuɗin yana da giɓin da sai gwamnati ta hada da rance za ta cike fiye da rabin sa, wanda ya kai tiriliyan 12.
Ministar Kuɗi Zainab Shamsuna ta ce gwamnati za ta cike giɓin ne ta hanyar ciyo bashi da kuma sayar da wasu kadarorin gwamnati.
Mene ne ra’ayin yan Nigeria game da wannan furuci na Ministan kudi.
Ku aje mana sakon ninku akan shafukanmu na Aksam Media concept.