Wani mutum ya datse mazakutarsa bayan kotu ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai. Mutumin mai suna Henry Hodges ya yanke wannan shawarar cikin bacin rai.
An yanke masa hukuncin ne bayan ya halaka wani mai gyaran waya a shekarar 1992. Ana zargin abinda ya hassala Henry shi ne yadda ya bukaci lauyansa ya kai masa abinci na alfarma a gidan yarin amma jami’ai su ka hana shi ci.
Da farko akan kisan da yayi, an yanke masa shekaru 40 ne, daga bisani kuma aka gane cewa shi ne ya halaka wani injiniya a wani otal da ke Atlanta.
Lauyansa ya kai masa ziyara Cibiyar Tsaro ta Riverbend Maximum a Nashville, inda ya je masa da abincin, sai dai an hana shi amsa.
An ga yadda Henry yayi bayan gida ya fara shafawa a bangon cikin gidan gyaran halin. Daga bisani kuma ya dauko reza a dakinsa inda ya fara yankar damtsensa a ranar 7 ga watan Oktoba.
Wani babban jami’i ya bukaci a mayar da shi daki bayan duba shi. Daga nan ne ya dauki reza a fasassun kwalabe inda ya guntule al’aurarsa gabadaya.
Yanzu haka jami’an sun samar da dakin da za a kebe shi a gefe guda, saboda kada ya zama hatsari ga kansa da wasu daban. Sannan kuma kada a dinga daure shi t amkar dabba.