A makon da ya gabata ma an yi irin wannan zargi cewa China ta buɗe ofishin a Najeriya da wasu ƙasashe.
Wata kafar yaɗa labarai ta Netherlands ɗin ta gano cewa “ofisoshin ƙasar wajen”, wadda ta ce za su yi aikin difilomasiyya, ana amfani da su ne wajen toshe bakin ‘yan adawar China.
Wata mai magan da yawun ma’aikatar harkokin waje ta Netherlands ta ce kafa ofisoshin ba a hukumance ba sun saɓa wa ƙa’ ida.
Ma’aikatar harkokin wajen China ta musanta zargin.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen China Wang Wenbin ya faɗa ranar Laraba cewa abin da aka siffanta da ofishin ‘yan sanda a ƙasashen waje “ofisoshin hidima ne ga ‘yan China”, kuma China na mutunta ‘yancin sashen shari’a na ƙasashe.
Yanzu aiki na kan gwamnatin Netherlands don tabbatar da cewa ta kare masu sukar China da ke neman mafaka a ƙasar.