Jihar Indiana da ke Amurka ta shigar da ƙara a kotu tana tuhumar kamfanin ByteDance wanda ya mallaki manhajar TikTok da nuna wa yara abubuwan da ba su dace ba.
An shigar da ƙarar ce a ranar Laraba ana zargin kamfanin da saɓa dokokin kare masu mu’amala da shi.
Babban mai shari’a na jihar Todd Rokita ya kuma zargi TikTok da ƙin bayyana yiwuwar cewa ƙasar China za ta iya tatsar bayanai ta manhajar.
Inda ya bayyana manhajar a matsayin ‘kura a cikin fatar akuya.’
Ƙarar ta ce tsarin na TikTok na tura wa yara bidiyon da ya ƙunshi shan kayan maye, da ƙwaya, da tsiraici, da lalata da kuma munanan kalamai.