Amurka ta Ɗauki hanyar rasa ko faduwa a gasar da take yi da China a nahiyar Afirka.  

Afirka ita ce nahiyar gaba. Ita ce kaɗai yankin duniya da ake ci gaba da samun ƙaruwa mai yawa a yawan jama’a. Ana sa ran zuwa shekarar 2050 Afirka za ta karɓi mutane biliyan 2.5. A wannan shekara kuma, ana tsammanin tattalin arziƙin Afirka zai haɓaka da kashi 4.4.

Wannan yana nuna cewa Afirka babbar kasuwa ce ta gaba, kuma nan gaba za ta taka muhimmiyar rawa a siyasar duniya.
Za a yi tsammanin manyan ƙasashen duniya biyu—Amurka da China—za su yi aiki tare da Afirka domin samar da ribar juna da warware matsaloli na bai ɗaya. Amma bambancin yadda suke mu’amala da Afirka ya yi yawa ƙwarai.

Tattalin Arziƙi:
Kusan dukkan ƙasashen Afirka—ban da Lesotho—sun fi yin ciniki da China fiye da Amurka. A shekarar 2025, China ta buɗe ciniki ba tare da haraji ba (zero tariff) ga dukkan ƙasashen Afirka. A gefe guda kuma, Amurka ta kafa sabbin shingayen kasuwanci, har ma da ƙasashen da suka fi talauci.

Amurka na rage tallafin da take bai wa Afirka, yayin da shirin China na Belt and Road Initiative ke zama muhimmin ginshiƙi wajen bunƙasa ci gaban Afirka.
Girmamawa:

Yawanci Amurka na bayyana hulɗarta da Afirka ne a matsayin wata hanya ta “dakile China”. Amma China na gabatar da hulɗarta da Afirka a matsayin haɗin gwiwa na moriyar juna. Afirka ba ta son zama filin wasa na manyan ƙasashe daga nesa.
Ziyara:

Ministan harkokin wajen China, Wang Yi, ya fara wannan shekara da ziyarar ƙasashe huɗu a Afirka. Wannan al’ada ce da China ke yi tsawon shekaru 36, inda manyan jami’anta ke fara sabuwar shekara da ziyartar Afirka. A bangaren Amurka kuwa, ziyarar manyan jami’an siyasa zuwa Afirka ta yi ƙasa sosai.

Shugaban China, Xi Jinping, ya ziyarci Afirka sau biyar tun bayan hawansa mulki. Amma banda ziyarar da Shugaba Biden ya kai bayan jam’iyyar Democrats ta rasa mulki, babu wani shugaban Amurka da ya ziyarci Afirka tun 2015. Shugaba Donald Trump kuma bai taɓa ziyartar Afirka ba.
Soja:

Amurka na kai hare-haren bom a Najeriya da Somaliya, amma ba tare da wani gagarumin sakamako ba. China kuwa ba ta tsoma baki a yaƙe-yaƙe a Afirka.
Gine-gine da Ababen More Rayuwa:
China ta gina layin dogo daga Mombasa zuwa Nairobi a Kenya, da kuma layin dogo tsakanin Habasha da Djibouti, tare da layukan tram a Addis Ababa. Kwanan nan China ta sanar da shirin farfaɗo da layin dogo na Tanzania–Zambia, sannan ana ci gaba da ayyuka a Najeriya. China ta kasance babbar ƙasa wajen gina hanyoyi da layukan dogo a Afirka.

Shugaba Biden ya sanar da cewa Amurka za ta taimaka wajen gina Lobito Corridor daga Angola zuwa Zambia. Amma ana ganin ba zai samu nasara ba, saboda babu kamfanoni masu zaman kansu da za su iya ɗaukar nauyin aikin, kuma da yawa na shakkar ko Shugaba Trump zai ci gaba da aiwatar da shirin da ya gada daga Biden.
Biza (Visa):

Amurka ta sanar da buƙatar ajiya tsakanin dala 5,000 zuwa 15,000 ga baƙi daga ƙasashen Afirka 24. Haka kuma, an haramta wa matafiya daga wasu ƙasashe shiga Amurka gaba ɗaya. Wannan zai kawo cikas ga ciniki da hulɗar siyasa.
Babu wata ƙasa a Afirka da ke son zaɓar tsakanin China da Amurka. Duk ƙasashen Afirka na son yin ciniki da ƙasashen biyu, tura ɗalibai zuwa can, yin haɗin gwiwa a siyasa, da ƙarfafa hulɗar jama’a tsakaninsu.

Bai kamata a samu gasa tsakanin Amurka da China a Afirka ba. Nahiyar tana da faɗi, kuma akwai damar cin moriyar juna marar iyaka. To amma me ya sa Amurka ke rufe ƙofofinta ga Afirka tare da barin nahiyar gaba ɗaya a hannun China?

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments